Talk:Andrzej Gąsienica-Makowski

Latest comment: 4 years ago by Darakta1988 in topic kano

kano edit

babbar kotu a jihar Kano ta dakatar da Gwamna

Abdullahi Ganduje daga kafa Majalisar Sarakunan jihar da kuma nada 'yan majalisar. Kotun ta bayar da umarnin ne kwana biyu bayan gwaman ya nada Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin shugaban Majalisar Sarakunan jihar tare da umartar sarkin ya kira taron majalisar ba tare da bata lokaci ba. Wasu na ganin matakin da gwamnan ya dauka a matsayin kokarin gyara alaka tsakaninsa da masarautar ta Kano. To amma masu lura da al'amura na ganin matakin a matsayin daure Sarki Sanusi da jijiyar jikinsa. Mene ne yake tsakanin Ganduje da mawakan Kannywood? Abin da sabuwar dokar masarautun Kano ta kunsa Martanin Sarki Sanusi kan sace yara ya bar baya da kura Rikicin Ganduje da Sarki Sanusi ya fara cin rawuna Sai dai wasu masu kusanci da fadar na cewa fadar ba ta samu sanarwar nada Sarki Sanusi a matsayin shugaban Majalisar Sarakunan jihar a hukumance ba. Hukuncin na kotu dai ya kuma hana gwamna yin wani aiki da bisa al'ada masu zabar sarkin Kano ke yi, har sai kotun ta saurari karar da aka shigar gabanta. Kotun ta sanya ranar 17 ga watan Disambar nan domin sauraron bangarorin da karar ta shafa. A makon jiya ne gwamnan ya sanya hannu a kan sabuwar dokar kafa sabbin masarautu hudu masu daraja ta daya, bayan kotu ta soke dokar farko da Majalisar jihar ta yi, inda ta bayyana ta a matsayin haramtacciya da aka yi ba bisa ka'ida ba. Masu nada sarki a Masarautar Kano ne suka sake kai karar Gwamna Abdullahi Ganduje da Majalisar Dokoki da gwamnatin jihar gaban kotu, abin da ke alamta har yanzu da sauran rina a kaba kan batun kafa sabbin masarautu a jihar. Madakin Kano da Makaman Kano da Sarkin Dawaki Mai Tuta da kuma Sarkin Ban Kano ne suka shigar da karar a gaban kotun. Masu shigar da karar na neman kotun ta dakatar da gwamnan da majalisar da kuma gwamnatin jihar da ma kwamishinan shari'a na jihar, daga yin kowane irin abu da ya shafi sabuwar dokar masarautun jihar. Suna kuma neman kotun ta hana wadanda ake karar tattunawa ko karatu ko mahawara ko amincewa ko rattaba mata hannu a kan sabuwar dokar har sai kotu ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar a kan lamarin. Sauran wadanda ake karar sun hada da shugaban majalisar dokokin jihar da sarakunan sabbin masarautun Bichi da Gaya Karaye da kuma Rano, wadanda a baya kotu to soke nadin da gwamnatin jihar ta yi musu. 'Yan majalisar sarkin da ke bukatar kotun ta umurci bangaren da su bar al'amura a yadda suke kafin kafa sabuwar dokar na zargin gwamnatin jihar da yi wa umurnin kotu karan-tsaye. Suna kafa hujja ne da abin da suka kira azarbabin bangaren ta bakin wani hadimin gwamnan na sanar da cewa zai ci gaba da daukar sarakunan da kotu ta soke a matsayin halartattu. Gwamnatin jihar ta sanar da hakan ne jim kadan bayan kotu ta soke sabuwar dokar da ta kafa sabbin masarautunsu saboda rashin bin ka'idojin majalisar wurin zartar da ita. Bayan nan ne gwamnatin jihar ta gabatar da dokar ga majalisar dokokin jihar, wadda ta yi mahawara kuma ta zartar da ita a zauren majalisar, bayan kotu ta dakatar da su daga sabunta dokar da ta kafa masarautar mai dadadden tarihi. Mai shari'a Ahmad Badamasi ya dage sauraron karar zuwa ranar Talata 17 ga watan Disambar na. Ya zuwa yanzu dai bangaren gwamnatin jihar da sauran wadanda ake kara ba su ce komai game da sabuwar karar da aka kai su ba. A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamna Ganduje ya nada Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan jihar, bayan gwamnan ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar masarautun jihar, mai cike da rudani. — Preceding unsigned comment added by Darakta1988 (talkcontribs) 21:45, 11 December 2019 (UTC)Reply